Hukumar Shirya Jarrabawar Kammala Sakandire ta Afirka ta Yamma, WAEC ta saki sakamakon ɗalibai 1,020,519 da suka zauna jarrabawar bana ta May/June 2019.
Olu Adenipekun, Shugaban Ofishin WAEC na Najeriya ya bada waɗannan alƙaluma yayinda yake sanar da fitar da sakamakon a wani taron manema labarai a Legas ranar Juma’a.
Ya ce an ɗan samu ci gaba a ƙwazon ɗalibai a jarrabawar 2019 idan aka kwatanta da ta 2018.
Mista Adenipekun ya ce ɗalibai 1,596,161 ne suka yi rijistar yin jarrabawar daga makarantun sakandire 18,639 da aka amince da su.
Ya ce ɗalibai 1,590,173 ne suka zauna jarrabawar daga cikin ɗaliban da suka yi rijistar.
A ta bakinsa, jimillar ɗalibai 1,309,570 sun samu ‘credits’ zuwa sama a darussa biyar, da darasin Turanci ko Lissafi.
Mista Adenipekun ya ce an riƙe sakamakon ɗalibai 180,205 da suka zauna jarrabawar bisa samun su laifukan maguɗin jarrabawa.
Ya faɗa wa manema labarai cewa ana kan bincikar waɗannan laifukan maguɗin jarrabawa, yana mai ƙarawa da cewa za a gabatar wa Kwamitin Hukumar rahoton binciken don ɗaukar matakin da ya dace.
“Za a sanar da ɗaliban da abin ya shafa hukuncin kwamitin ta hanyar makarantunsu”, in ji shi.
Ya ce an gama fitar da sakamakon ɗalibai 1,468,071, yayinda ake ci gaba da haɗa sakamakon 122,102.
Mista Adenipekun ya bada tabbacin cewa ana ci gaba da ƙoƙarin ganin an saki sakamakon sauran ɗaliban da ba a saki nasu ba.
Ya ce ɗalibai 299 daga cikin ɗaliban da suka zauna jarrabawar makafi ne, 842 kuma kurame ne, 158 suna gani garara-garara, 75 nada matsalar ƙwaƙwalwa, sai 85 guragu.
“Dukkan waɗannan ɗalibai masu buƙata ta musamman an samar musu da abubuwan da suke buƙata a yayin gudanar da jarrabawar.
“An kammala duba sakamakon waɗannan ɗalibai, an kuma sake shi tare da na sauran ɗalibai”, in ji shi.
Ya ce an ɗora bayanin sakamakon jarrabawar filla-filla a Intanet.