Gwamnatin Jihar Jigawa ta buɗe damar karɓar takardun neman kwangila don gina wa masallaci na Miliyan 57 a Jami’ar Gwamnatin Tarayya dake Dutse, FUD.
Alhaji Isma’il Ibrahim, mai magana da yawun Ofishin Sakataren Gwamnatin Jihar, SSG ya bayyana haka a wata sanarwa da ya bayar a Dutse.
Sanarwar ta ce Alhaji Muhammad Dagaceri, Babban Sakatare a Ofishin SSG, ya sanar da wannan ci gaba yayinda yake gina harsashin gina masallacin a Dutse ranar Alhamis.
Sanarwar ta ce kamfanoni uku ne suke gasar neman kwangilar.
Ta ƙara da cewa a jawabinsa, wakilin Hukumar Tabbatar da Bin Ƙa’ida a Aikin Gwamnati da Duba Ayyuka ta Jihar Jigawa, Nura Jibo, ya tabbatar wa da ‘yan ƙwangilar cewa Technical Evaluation Committee da za a kafa zai yi adalci gare su.
Wakilin Kamfanin Gine-gine na Modgan Investment Ltd, Alhaji Garba Isama’i, wanda ya yi magana a madadin sauran ‘yan kwangilar ya tabbatar wa da Gwamnatin Jihar cewa za su kammala aikin a kan lokaci.