Kotu ta bayyana Ƙungiyar ‘Yan Shi’a a matsayin ta ‘yan ta’adda

161

Babbar Kotun Tarayya dake Abuja a Najeriya ta bayyan Ƙungiyar Islamic Movement of Nigeria, IMN da aka fi sani da Shi’a a matsayin ƙungiyar ‘yan ta’adda, ta kuma bada umarnin a haramta aikace-aikacenta.

Umarnin da Mai Shari’a Nkeonye Maha ya biyo bayan buƙatar da Gwamnatin Tarayya ta shigar mai lamba FHC/ABJ/CS/876/2019, waddda Ministan Shari’a na Ƙasa ya shigar, kamar yadda jaridar PUNCH mai fitowa ranar Asabar ta ruwaito.

“Gwamnatin Tarayyar ta shigar da buƙatar ne a gaban kotun ranar Alhamis, sa’o’i 72 bayan wata zanga-zanga da ‘yan Shi’ar suka yi a Abuja ta haifar da zubar da jini tsakaninsu da ‘yan sanda”, in ji rahoton.

Sanarwar ta ce Mataimakin Kwamishinan ‘Yan Sanda Mai Kula da Aikace-aikace a Rundunar ‘Yan Sanda ta Birnin Tarayya, Abuja, Nyinnaya Adiogu, wanda ya zama wakili a wajen shigar da ƙarar, ya yi zargin cewa ‘yan Shi’a sun shiga abubuwa daban-daban, “waɗanda sun saɓa da kasancewar Najeriya ƙasa ɗaya”.

Mai Shari’a Maha ya amince da roƙo huɗu dake cikin buƙatar jim kaɗan bayan Babban Lauyan Ƙasa kuma Babban Sakataren Ma’aikatar Shari’a ta Ƙasa, Mai Shari’a Dayo Apata ya gabatar da buƙatar ranar Juma’a.

Kotun, a cewar Jaridar PUNCH Mai fitowa ranar Asabar, ta hana: “Duk wani mutum ko wasu gungun mutane daga shiga duk wasu aikace-aikace da suka haɗa ko suka shafi IMN da kowane irin suna ko jami’yya a Najeriya.

Don kammala shirin haramta ƙungiyar, kotun ta umarci Ministan Shari’a na Ƙasa da ya “wallafa umarnin haramta wadda ake ƙara (Islamic Movement of Nigeria) a mujallar gwamnati da manyan jaridun ƙasa guda biyu”.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan