Rundunar ‘Yan Sandan Kano ta kashe wani ƙasurgumin ɗan fashi

19

Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kano ta ce ta kashe wani mamba na ƙungiyar ‘yan fashi wanda ba ta bayyana sunansa ba, wanda ya riƙa addabar garin Rano dake kan Dajin Falgore.

Jami’in Huɗɗa da Jama’a na Rundunar, DSP Abdullahi Haruna ya bayyana haka ranar Asabar a Kano.

Ya ce kisan ya biyo bayan musayar wuta da aka yi tsakanin jami’an ‘yan sanda na Operation Puff-Adder da ‘yan fashin.

Mista Haruna ya ce ranar 26 ga watan Yuli da misalin ƙarfe 3:40 na dare, aka ankarar da wasu jami’an ‘yan sanda na Operation Puff-Adder dake aiki da Rundunar ‘Yan Sanda ta Yankin Rano cewa wasu ‘yan fashi su huɗu sun kai wa mazauna Rano hari.

Ya ce nan da nan sai ‘yan sanda suka garzaya zuwa wajen, inda suka yi ɗauki ba daɗi da ‘yan fashin.

Mista Haruna ya ce a yayin ɗauki ba daɗin, jami’an ‘yan sanda na Operation Puffe-Adder, waɗanda ke da manyan bindigogi da suka fi na ‘yan fashin, suka kashe ɗaya daga cikin ‘yan fashin, yayinda sauran ukun suka tsere zuwa dajin dake kusa.

“A wannan ba-ta-kashi, ‘yan fashin suka bar wata bindiga ƙirar gida da albarusai uku”, in ji shi.

Mista Haruna ya ƙara da cewa waɗannan ‘yan fashi sun riƙa addabar Rano, Kibiya, Bunkure, Tudun Wada dake kusa da Dajin Falgore na ɗan wani lokaci.

Ya ce Kwamishinan ‘Yan Sanda na Jihar Kano, Ahmed Iliyasu ya bada umarnin a gano inda sauran ‘yan fashin uku da suka tsere suke a kan lokaci, a gane su kuma a cafke su.

Ya ce Mista Iliyasu ya kuma bada umarnin a ƙwace duk wani makami dake hannun ‘yan fashin.

Mista Haruna ya yi kira ga al’ummar Jihar Kano da su ci gaba da ba ‘yan sanda haɗin kai wajen ba su bayanai da rahotannin sirri game da kowane irin laifi a faɗin jihar don ɗaukar mataki a kan lokaci.

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan