Abba Kabir Yusuf na ci gaba da yin nasara a kotu

124

Kotun Ɗaukaka Ƙara dake Kaduna ta amince da buƙatar da jam’iyyar PDP da ɗan takararta na gwamna, Abba Kabir Yusuf suka shigar gabanta, inda suke roƙon a ba su damar gabatar da shaidun da ba su rubuta a jerin shaidunsu ba.
Wata sanarwa da mai magana da yawun Abba Kabir Yusuf ya sanya wa hannu ta ce an shigar da ƙarar ne bayan hukuncin 16 ga watan Yuli na Kotun Sauraron Ƙorafe-ƙorafen Zaɓen Gwamna ta Kano cewa PDP da ɗan takararta ba za ta iya gabatar da shaudun da tun farko ba sa cikin waɗanda aka miƙa wa kotun ba.

A cikin shaudun takwas da ba a sa sunansu ba da akwai Shugaban Jam’iyyar PDP na Jihar Kano, Rabi’u Suleiman Bichi.
A safiyar Litinin ɗin nan ne Mai Shari’a A.O Okoji ta karanta hukuncin kotun a madadin alƙalan biyar.

Waɗanda ake ƙara, Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa, INEC, jam’iyyar APC da Gwamna Ganduje sun sha alwashin ɗaukaka ƙara a Kotun Ƙoli dake Abuja.

A martaninsa a madadin Abba Kabir Yusuf, Bashir Yusuf Tudun Wazirici ya ce sun tunkari kotun da fatan samun nasara

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan