Buhari da Oshiomhole sun yi ganawar sirri

122

A ranar Litinin ɗin nan ne Shugaba Muhammadu Buhari zai yi wata ganawar sirri da Shugaban Jam’iyyar APC na Ƙasa, Adams Oshiomhole.

Mista Oshimohole ya isa Fadar Shugaban Ƙasa dake Abuja da misalin ƙarfe 3:25, tattaunawar tasu ta sirri kuma ta fara a Ofishin Shugaban Ƙasa da misalin 3:30.

Koda yake dai ba a san dalilin haɗuwar tasu ba, amma rahotanni sun ce ba za ta rasa nasaba da rikice-rikicen APC da kuma yadda aka samu kiki-kaka bayan fitowar sunayen ministoci ba.

An ci gaba da tattaunawar har bayan ƙarfe 4.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan