Masu siyar da jarida a Anambra sun shiga yajin aiki bisa zargin gwamnati da takura musu

165

A ranar Litinin ɗin nan ne masu siyar da jarida a Awka, babban birnin jihar Anambra suka fara wani yajin aikin sai baba ta gani bisa zargin cewa gwamnatin jihar ta takura musu.

Wakilin Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya, NAN, wanda ya ziyarci wajen da ‘yan jaridar ke siyar da jarida a Mahaɗar UniZik, Aroma da kuma daura da Ofishin ‘Yan Kwana-kwana, Anawbia, ya ruwaito cewa bai ga jarida ko ɗaya ba a wuraren biyu.

Ƙungiyar Dillalan Jarida ta Najeriya, Reshen Awka, a wani ƙorafi da ta rubuta wa Sakataren Gwamnatin Jihar, ta yi iƙirarin cewa ana cin zarafin mambobin nata tare da razanar da su.

Takardar ƙorafin wadda aka raba wa manema labarai, ta samu sa hannun Muƙaddashin Shugaban Ƙungiyar, Emeka Nweze da kuma Sakataren Ƙungiyar, Ifeanyi Nwafor.

Ƙungiyar ta yi zargin cewa jami’an Operation Clean and Anambra State Healthy Brigade, OCHA suna tatsar kuɗi daga masu siyar da jaridun.

“Dillallan jarida da masu tallar ta sun riƙa shan wahala daga hannun jami’an OCHA Brigade tsawon lokaci”, in ji ƙungiyar.

“Jami’an sukan ƙaddamar mana, suna razanar da mu tare da ci mana zarafi, suna ƙwace abubuwan da muke amfani da su wajen tallata jarudunmu, wasu lokutan ma sukan tatsi kuɗaɗe daga gare mu.

Ta ƙara da cewa mambobin suna gudanar da sana’arsu ne a wuraren da Hukumar Kula da Tsaftar Muhalli ta Jihar Anambra ta amince.

A cewar ƙungiyar, gwamnati ta ƙwace kayan masu siyar da jaridun da kuɗinsu ya haura N70,000 a watanni uku da suka gabata.

Ƙungiyar ta ce mambobinta za su daina raba jaridu da mujallu a yankin har sai gwamnatin jihar ta tabbatar musu da tsaro.

Misis Nneka Okeke, wata mai siyar da jarida a Mahaɗar Aroma ta faɗa wa NAN cewa masu wallafa jarida sun kawo jaridun Awka, amma mambobin sun ƙi su raba saboda yajin aiki.

Tony Maduforo, wani wanda ya saba siyan jarida ya ce baƙon abu ne a ce masu siyar da jarida sun tsunduma yajin aiki saboda yadda aikin nasu yake, ya yi kira ga gwamnati da ta sa baki a lamarin.

NAN ya bada rahoton cewa duk ƙoƙarin jin ta bakin Shugaban OCHA Brigades, Douglas Okafor ya ci tura saboda wayarsa a kashe take.

Amma lokacin da aka tuntuɓi Kwamishinan Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Al’umma na Jihar Anambra, C-Don Adinuba ya ce zai kai maganar wajen Shugaban OCHA Brigade da nufin warware matsalar cikin gaggawa.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan