Gwamna Zulum ya dakatar da wasu likitoci bisa rashin samun su a bakin aiki

182

Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya bada umarnin da a dakatar da Shugaban Asibitin Umaru Shehu Ultra Modern Hospital da wasu likitoci huɗu waɗanda ba sa bakin aiki lokacin da ya kamata a ce suna bakin aikin.

Idan dai za a iya tunawa, Labarai24 ta kawo muku labarin yadda Gwamna Zulum ya kai ziyarar bazata a asibitocin a ranar Litinin da tsakar dare da misalin ƙarfe 2, inda ya samu cewa daga cikin likitoci masu neman ƙwarewa 19 dake asibitin ba wanda ke aiki a lokacin.

Wata sanarwa da aka fitar ranar Laraba ta ce: “Gwamna Zulum ya bada umarnin da a dakatar da Shugaban Asibitin Umaru Shehu Ultra Modern Hospital, Dokta Audu Usman, bisa gazawar sa ta shugabanci.

“Sauran likitocin da dakatarwar ta shafa sun haɗa da Musa Chuwang da Dokta Chijioke Ibemere waɗanda su ma ba sa nan, su ma an dakatar da su.

“Dokta Baba Ali Malgwi, wanda shi ne mutum na biyu da ya kamata a ce yana bakin aiki, an dakatar da shi saboda gazawar sa wajen amsa kiran waya lokacin ziyarar Gwamnan.

“A lokacin ziyarar, duk ƙoƙarin samun su bai yi nasara ba, duk da cewa yana zaune a gidan likitoci dake cikin asibitin.

“Haka kuma, an samu cewa Dokta Esther ta Sashin Kula da Ƙashi, ba ta bakin aiki, duk da ya kamata a ce tana bakin aikin, ita ma an dakatar da ita.

“Dukkan likitocin dake sashin haɗari da kulawar gaggawa an ba su takardun tuhuma bisa rashin zuwa aiki da rashin takardar tsarin zuwa aiki.

“Ana umartar Shugaban Hukumar Kula da Asibitoci ta Jihar Borno da ya bi wannan umarni na Gwamna, ya kuma ɗauki matakan ganin cewa an cike dukkan guraben.

“Gwamna Zulum a shirye yake wajen tabbatar da cewa dukkan asibitoci a faɗin jihar Borno suna samar da isasshiyar kulawa a koyaushe”.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan