Sabon Shugaban Pillars Yace Asante Kotoko Na Tsoron Pillars

155

Sabon shugaban kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars wato Alhaji Surajo Sha’aibu Yahaya ya bayyana cewar kungiyar kwallon kafa ta Asante Kotoko ta kasar Ghana tana tsoron Kano Pillars awasan dazasu fafata.

Yayi wannan bayani ne lokacin dayake ganawa da ‘yan wasan na Kano Pillars a jahar Kaduna inda suke daukan horo.

Yakara da cewar kungiyoyin kwallon kafa da dama a Najeriya suna tsoron Kano Pillars.

Aranar 10 ga watane idan Allah ya kaimu Kano Pillars zasu fafata da kungiyar kwallon kafa ta Asante Kotoko awasan farko na gasar zakarun nahiyar Afrika.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan