Liverpool Da Man City Ko Guardiola Da Joggin Klopp

140

A yau za a fafata wasa tsakanin kungiyar kwallon kafa ta Manchester City da Liverpool wato kofin Community Shield.

Manchester City ne suka lashe duk wasu kofunan kasar Ingila inda Liverpool ne sukayi matsayi na biyu.

Daman biaa al’adar kasar Ingila mako guda kafin afara gasar Premier ake buga wannan kofin.

Za a buga wannan wasa da misalin karfe 3 agogon Najeriya.

Amma saidai a ‘yan shekarun nan za a iya cewa Liverpool suna yawan samun nasara akan Manchester City.

Kuma a dukkanin masu horas wa na duniya babu wanda yazamewa Guardiola gagarabadau kamar Klopp, domin kusan ko yaushe ragargazar Guardiola yakeyi.

Shin ko yaya zata kasance ayau tsakaninsu? Liverpool ne ko Man City, a’a Guardiola ko Joggin Klopp?

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan