Zuwan Pep Guardiola Manchester City Yazama Gagarabadau

155

Tun bayan da mai horas wa Pep Guardiola yake kungiyar kwallon kafa ta Manchester City dake kasar Ingila nasara take ta barkowa kungiyar tako ina inda yake nema yazama gagarabadau amma a kasar Ingila.

Ga yadda abin yake kamar haka:

Pep Guardiola ya jagoranci wasanni 175 a Manchester City, ya lashe wasanni 132, inda ya buga kunnen doki guda 20 yayi rashin nasara a wasanni guda 23.

Haka zalika daga cikin wasannin daya jagoranta kungiyar ta Manchester City ta jefa kwallaye 450 inda aka jefamata guda 154.

Ayanzu haka Guardiola ya tara maki 413 a kungiyar kwallon kafan ta Manchester City.

Sannan ya lashe kofuna 7 a kungiyar ta Manchester City.

Shin ko Guardiola zaici gaba da kafa tarihi a kungiyar kwallon kafan ta Manchester City?

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan