Za a fara Sabuwar Kakar Wasan Premier Ta Ingila A Yau

159

A yau Juma’a 9 ga watan Augusta za a fara wasan farko na kakar wasan ajin Premier ta kasar Ingila wato 2019 zuwa 2020.

Inda za a fara wasan farko tsakanin kungiyar kwallon kafa ta Liverpool da Norwich a filin wasa na Anfield da misalin karfe 8:00 na daren yau agogon Najeriya.

Kungiyoyin kwallon kafa dai sunyi cefane a kasar ta Ingila a wannan kakar wasan daza a shiga a yau.

Saidai za a iya cewa wasu sunyi cefane mai kyau inda wasu kuma cefanen kamar basuyi mai kyau ba.

Amma sai an fara gasar sannan za a gane wadanda sukayi cefane mai kyau.

Kungiyar kwallon kafa ta Manchester City dai sun lashe gasar sau 2 a jere, shin ko zasu maimaita hawa na 3 a bana ma’ana su dauki na 3 a jere? Kokuwa za a takamusu birki?

A wasan farkon dai na yau tsakanin kungiyar kwallon kafa ta Liverpool da Norwich alkalin wasa Michael Oliver ne zai jagoranci wasan tare da masu taimakamasa wato Stuart Burt da Simon Bennett.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan