Home / Gwamnati / Ganduje ya hana Hakimai zuwa Hawan Daushe

Ganduje ya hana Hakimai zuwa Hawan Daushe

Gwamnan Jihar Kano, Dakta Abudullahi Umar Ganduje ya hana Hakimai 36 daga cikin 44 halartar Hawan Daushe da Sarkin Kano ke yi kwana ɗaya da yin Sallah a Kano.

Wata sanarwa daga Mista Ganduje ta ci karo da wata sanarwa da Majalisar Masarautar Kano ta fitar a gidajen rediyon jihar, inda take gayyatar dukkan Hakimai su halarci Hawan Daushen.

Idan dai za a iya tunawa, Mista Ganduje ya sanya wa wata doka hannu, wadda ta kafa ƙarin masarautu huɗu da Sarakuna masu Daraja ta Ɗaya a Rano, Bichi, Ƙaraye da Gaya.

Akwai ƙararraki biyu da aka shigar kotu, waɗanda ke ƙalubalantar kafa sabbin masarautun.

Matakin na Ganduje ya rage wa Sarki Sanusi tasiri a sarautar Kano.

Gwamna Ganduje ya umarci Hakiman da su yi watsi da umarnin Sarkin, su kuma tafi masarautunsu daban-daban don yin Hawan Daushen.

About Hassan Hamza

Check Also

Rugujewar Kwankwasiyya ta kunno kai a jihar Kano – Fa’izu Alfindiki

Fitaccen mai adawa da tsarin siyasar tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso kuma …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *