Jam’iyyar PDP ta lashe zaɓe a dukkan ƙananan hukumomi takwas na Jihar Bayelsa a zaɓen da Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Jihar Bayelsa, BASIEC, ta gudanar ranar Asabar.
Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya, NAN ya ruwaito cewa Bayelsa nada ƙananan hukumomi takwas ne.
Jam’iyyar APC ba ta shiga zaɓen ba saboda abinda ta yi zargi na rashin bin ƙa’ida.
Jami’in Sanar da Sakamakon Zaɓe, Frank Ebikumor, ya sanar ranar Lahadi a Yenagoa cewa Dengiye Ubarugu na jam’iyyar PDP ya samu kuri’a 42,539 inda ya doke jam’iyyar ADC, waddda ɗan takararta ya samu kuri’a 1,031 a Ƙaramar Hukumar Kololuma/Opokuma.
A Ijaw ta Kudu, Jami’in Sanar da Sakamakon Zaɓe, Nwiwu Johnson, ya sanar da cewa Nigeria Kia na jam’iyyar PDP ya samu ƙuri’a 107,150 inda ya doke ɗan takarar ADC, wanda ya samu ƙuri’a 2,489.
A Ƙaramar Hukumar Ekeremor, Jami’in Sanar da Sakamakon Zaɓe, Dokta Victor Ayibatonye, ya sanar da Chif Perekeme Petula na PDP a matsayin wanda ya lashe zaɓe da ƙuri’a 62,529, inda ɗaya jam’iyyar ba ta samu komai ba.
Haka kuma, a Ƙaramar Hukumar Sagbama, wadda Gwamna Seriake Dickson ya fito daga cikin ta, Jami’in Sanar da Sakamakon Zaɓe, Dokta ThankGod Apere,ya sanar da Alah Embeleakpo a matsayin wanda ya lashe zaɓe da ƙuri’a 96,468, yayinda sauran jam’iyyu suka rasa ƙuri’u.
A Ƙaramar Hukumar Brass, Jami’in Sanar da Sakamakon Zaɓe, Timothy Ogiaba, ya sanar da Victor Isaiah na jam’iyyar PDP a matsayin wanda ya yi nasara da ƙuri’a 28,667 yayinda jam’iyyar LP ta samu ƙuri’a 2,948.
A Ƙaramar Hukumar Ogbia, Ebiye Ogoli, Jami’in Sanar da Sakamakon Zaɓe, ya sanar da Turner Ebinyo na jam’iyyar PDP a matsayin wanda ya yi nasara da ƙuri’a 17,661, inda ya kayar da ADC, waddda ta samu ƙuri’a 1,017.
A Yenagoa, Jami’in Sanar da Sakamakon Zaɓe, Dokta Good-head Abraham, ya bayyana cewa Uroupaye Nimizuoa na jam’iyyar PDP ya samu ƙuri’a 98,831 inda ya doke Kwokwo na ADC, wanda ya samu ƙuri’a 636.
A jawabinsa, Dokta Remember Ogbe, Shugaban BYSIEC ya ce an gudanar da zaɓen cikin lumana a dukkan yankunan Jihar Bayelsa.