Sarkin Gwandu ya bayyana dalilan da suka sa Najeriya ke fuskantar rashin tsaro

120

Sarkin Gwandu kuma Shugaban Majalisar Sarakunan Kebbi, Muhammadu Bashar, ya bayyana cewa yawaitar luwaɗi, fyaɗe da maɗigo su ne dalilan dake kawo rashin tsaro a ƙasar nan.

Basaraken ya bayyana haka ne yayinda yake yi wa talakawansa jawabin Babbar Salla a Birnin Kebbi ranar Lahadi.

A ta bakinsa, halin rashin tsaro da ake fama da shi a halin yanzu yana da dangantaka da yadda ‘yan Najeriya ke watsi da umarnin Ubangiji, suka kuma riƙi halayen Shaiɗan.

“Al’ummar wannan zamani tana fama da matsalolin fyaɗe, luwaɗi, maɗigo, garkuwa da mutane da yawan kashe-kashe, waɗanda ke haifar da rashin tsaro da Najeriya ke fuskanta a yanzu”, in ji shi.

Ya roƙi al’umma da su dasa wa ‘ya’yansu tarbiyya da girmama jama’a ta hanyar ba su ilimi mai inganci.

“Ina godiya ga Ubangiji bisa ba mu damar ganin wata Sallar.

“Matsalolin da al’ummarmu ke fama da su a halin yanzu nada alaƙa da rashin tarbiyya da son duniya”, in ji Basaraken.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan