An Nada Sakataren NNF Dr. Sunusi Amatsayin Dan Masanin Wajeke a Sokoto

5

An nada sakataren hukumar kwallon kafa ta kasar nan wato Dr. Mohammed Sunusi a matsayin Dan Masanin Wajeke a Wamako dake jahar Sokoto.

Hukumar kwallon kafa ta babban birnin tarayya Abuja ta taya sakatare General na hukumar kwallon kafa ta kasar nan wato Dr. Sunusi murnar nadin sarautar Dan Masanin Wajek na Wamako dake jahar Sokoto.

An nada Dr. Sunusi a ranar Idin babbar Sallah wato Jiya kenan a jahar ta Sokoto domin jajircewarsa wajen farfado da wasanni tun daga tushe a jahar Kebbi.

Shi kansa shugaban hukumar kwallon kafan ta babban birnin tarayya Abuja Muhammad mukhtar dayake can kasa mai tsarki domin sauke farali ya taya Dr. Sunusi murna na wannan nadi da akayimasa.

Dr. Mohammed Sunusi yayi addu’ar neman zaman lafiya da hadin kai a jahar ta Sokoto dama kasa baki daya a lokacin da ake masa wannan nadin.

Dr. Sunusi shine yake daukan nauyin gasar Charity Cup ta jahar Kebbi a duk shekara.

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan