A ranar Litinin ɗin nan ne Hukumar Aikin Haji ta Ƙasa, NAHCON ta ƙaryata rahotannin dake zagayawa a soshiyal midiya cewa ta bar maniyyata 400 waɗanda suka yi rijista ta Jihar Kano.
Da yake yi wa manema labarai jawabi a Makka, a mayar da martani da ya yi game da zargin, Kwamishinan Aikace-aikace na NAHCON, Abdullahi Saleh, ya bayyana cewa Hukumar ba ta bar wani maniyyaci a ƙasa ba.
Amma, a ta bakinsa, maniyyatan da aka bari a ƙasa su ne waɗanda suka yi rijista da kamfanonin jiragen yawo.
Mista Saleh ya lura da cewa, saboda haka, dukkan maniyyata 44,450 waɗanda suka yi rijista da Hukumomin Jin Daɗin Alhazai na Jihohi an kai su Saudiyya kafin a rufe jigila ranar 4 ga Agusta, 2019.
Ya ce rukunin ƙarshe na maniyyata da suka zo Saudiyya a jirgin Flynas ba su kai 200 ba, jirgin da yakan iya ɗaukar fiye da fasinjoji 400.
Mista Saleh ya ce ba wani kamfanin shirya tafiye-tafiye da ya zo wajen NAHCON don yin ƙorafi game matsalolinsa kamar yadda Hukumar ta ba su shawara.
“Kamfanonin shirya tafiye na jiragen yawo suna da zaɓi mai faɗi wajen ɗaukar kamfanonin zirga-zirgar jiragen sama da za su ɗauki alhazansu. Sukan dogara da jirage masu tafiye-tafiye a duk mako.
“NAHCON ta ba su shawara da su bada bayanan kamfanonin jiragen sama da suke amfani da su a kan lokaci don a taimake su idan sun samu matsala.
“Ba su yi haka ba. Ba su ma zo NAHCON su ce wannan shi ne kamfanin jirgin sama da za mu yi amfani da shi ba.
“Ko yanzu da nake magana da ku, ba wani kamfanin jirgin sama na yawo da ya zo mu taimake shi don ya samu matsala.
“Abinda suka yi tsarinsu ne. Kamar yadda abin yake, sun zo a makare saboda haka wanda suka ce wajensa ma ba zai iya taimaka musu ba, saboda an kulle filin saukar jiragen sama na Saudiyya a hukumance ranar 4 ga Agusta”, ya ƙara da haka.
Amma, Hukumar ta ce , za a kare haƙƙin alhazai, tana mai ƙarawa da cewa za a hukunta masu laifin bayan kammala bincike.
Ya ce NAHCON ba za ta yi wata-wata ba wajen ƙaƙaba wa masu laifin takunkumi ta hanyar janye lasisinsu da gurfanar da su gaban kotu.
A ta bakinsa, wannan mataki zai zama darasi ga sauran kamfanonin jiragen yawo.
Ya ce daga cikin kujeru 20,000 da aka ba kamfanonin jiragen yawo, 19,800 suka yi rijista da su don zuwa Saudiyya.