Daga ƙarshe dai Zakzaky ya tafi Indiya don neman magani

147

Jagoran Ƙungiyar Islamic Movement of Nigeria, IMN, da aka fi sani da Shi’a, Ibrahim El-Zakzaky da matarsa sun tafi zuwa Indiya a jirgin Kamfanin Emirates a cikin jirgin Boeing 777-300ER mai lamba EK786 ranar Litinin ɗin nan da misalin ƙarfe 6:29 na yamma.

Daga cikin ‘yan tawagar jagoran na Shi’a da akwai matarsa, Zeenat; ɗansa, Mohammed; sai wata, Zainab Hamid; likitarsa, Ramatu Abubakar; jami’an tsaro na farin kaya, SSS guda biyu, da; wani likita ɗan sanda.

Jaridar PRNigeria ta jiyo daga majiyoyin tsaro cewa Shugaba Buhari ya sassauta wasu sharuɗɗai da Gwamnatin Jihar Kaduna ta gindaya wa El-Zakzaky kafin tafiyar tasa.

Hukumar Binciken Sirri ta Ƙasa, NIA da Hukumar Tsaro ta Farin Kaya, DSS, waɗanda suka yi ta ƙoƙari ta ƙarƙashin ƙasa don warware matsalar da tsare shugaban na Shi’a ta jawo su suka shawarci Fadar Shugaban Ƙasa bisa dacewar bin umarnin kotu tunda wasu ƙasashe wajen da suka haɗa da Iran sun sha alwashin bin hanyoyin Diplomasiyya don shawo kan batun.

Da yake yi wa PRNigeria jawabi game da wannan ci gaba na baya bayan nan, wani ɗan rajin kare haƙƙin ɗan Adam kuma lauyan Mista Zakzaky, Femi Falana, SAN, ya ce gwamnati ta yi watsi da tsauraran sharuɗɗan da Gwamnatin Jihar Kaduna ta sa kafin ƙyale Shugaban na Shi’a da matarsa su yi tafiyar don neman lafiya.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan