NAHCON ta bayyana adadin alhazan Najeriya da suka rasu

194

Shuganan Tawagar Likitocin Najeriya na Hukumar Aikin Haji ta Ƙasa, NAHCON, Dokta Ibrahim Kana, ya sanar da cewa adadin alhazan Najeriya da suka rasu a yayin gudanar aikin Haji na 2019 a Saudiyya ya kai tara.

Mista Kana ya bada sanarwar ne yayinda yake yi wa manema labarai jawabi game da aikace-aikacen Tawagar Likitocin ga alhazai.

“Wata Hajiyar Jihar Legas ta yanke jiki ta faɗi, an kawo ta asibiti a Muna, amma ta mutu. Hawan jini ta yi fama da shi”, in ji Mista Kana.

Da yake tattaunawa da wani wakilin Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya, NAN a Muna tun da farko, Shugaban Alhazan Jihar Legas, AbdulLateef Abdulkarim ya bayyana sunan marigayiyar da Folashade Lawal.

Ya ce marigayiyar, Misis Lawal ta fito ne daga Ƙaramar Hukumar Oshodi ta jihar, yana mai lura da cewa ta yanke jiki ta faɗi ne da misalin ƙarfe 3 na dare yayinda take shirin zuwa Jamrat don yin jifar Shaiɗan.

Jifar Shaiɗan yana ɗaya daga cikin ayyukan aikin Haji.

Shugaban ya ce Tawagar Likitocin ta buɗe ofisoshi 21 a Muna da isassun magunguna da motocin ɗaukar marasa lafiya.

Mista Kana ya ce an samar da isassun likitoci masu horo waɗanda ke kula da alhazai.

Ya bayyana mura da hawan jini a matsayin wasu daga cikin cutukan da suka fi damun alhazai.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan