Gwamnan Legas zai naɗa kwamishinoni daga ƙabilu daban-daban

215

Gwamnan Jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu, ya miƙa jerin sunayen kwamishinoninsa na biyu ga Majalisar Dokokin Jihar Legas don tabbatarwa inda ya bada sunan wani Bahaushe, Kabiru Ahmed da wani Ibo, Joe Igbekwe a matsayin kwamishinoni.

Ƙabilar Yarbawa, ɗaya daga cikin manyan ƙabilu uku na Najeriya da ake kira WAZOBIA su ke da rinjaye a Legas.

Wata sanarwa da mai magana da yawun Mista Sanwo-Olu, Gboyega Akosile ya fitar ranar Talatar nan ta ce jerin sunayen yana ƙunshe ne da sunaye 13.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya, NAN ya ruwaito cewa ranar 14 ga Yuni, Mista Sanwo-Olu ya miƙa sunayen mutane 25 ga Majalisar Dokokin Jihar a matsayin kwamishinoni da masu bada shawara na musamman don tabbatarwa.

Tuni Majalisar ta tantance sunayen mutanen na farko.

Mista Akosile ya ce sunayen da aka miƙa yanzu su haɗa da: Oladele Ajayi, Oluwatoyin Fayinka, Yetunde Arobieke, Olanrewaju Sanusi, Joe Igbokwe, Bonu Solomon Saanu, Kabir Ahmed da Lola Akande.

Sauran su ne: Anofi Elegushi, Solape Hammond, Moruf Akinderu Fatai, Shulamite Olufunke Adebolu da Tokunbo Wahab.

A cewar Mista Akosile, jerin sunayen na biyu yana ƙunshe da sunayen ‘yan siyasar da suka yi bajinta a siyasa, da gogaggun mutane da suka san buƙatun jihar da kuma ajanda ta ci gaba ta Gwamnan.

Ya ce an bi hanyar ba sani ba sabo wajen zaɓo sunayen kwamishinonin, saboda buƙatar da ake da ita na gina wata tawaga ta musamman da za ta yi wa Legas hidima, dai-dai da shirin Gwamnatin Sanwo-Olu na samar da wani birni da zai zama ɗaya daga cikin manyan biranen da ake rayuwa a cikinsu a duniya.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan