‘Yan Shi’ar Indiya sun yi tayin biya wa El-Zakzaky kuɗaɗen magani

11

Anjuman-e-Haideri, ƙungiyar ‘yan Shi’a ta Indiya ta yi tayin biyan dukkan kuɗaɗen maganin da Ibrahim El-Zakzaky, Shugaban Islamic Movement of Nigeria, IMN, wato Shi’a zai siya.

A ranar Talatar nan ne ne Shugaban Shi’ar da matarsa, Zeenat suka sauka a Indiya don duba lafiyarsa bayan wata Babbar Kotun Jihar Kaduna dake Najeriya ta ba shi izinin yin tafiya.

A halin yanzu, Mista El-Zakzaky yana kwance a Asibitin Medanta dake New Delhi.

A wata wasiƙa d Sakatare Janar na Anjuman-e-Haideri, Bahadur Naqvi ya sanya wa hannu, aka kuma aika wa Manajan Darakta kuma Babban Likitan Fiɗa na Asibitin Medanta, Dokta Naresh Trehan, ƙungiyar ta yi tayin biyan dukkan kuɗaɗen magani da Mista El-Zakzaky zai buƙata a Indiya.

Wasiƙar, mai ɗauke da kwanan watan 12 ga Agusta ta ce: “Maulana Ibrahim El-Zakzaky, wanda shahararren Shugaban Shi’a ne ta Musulunci, wanda yake da ɗimbin mabiya a faɗin duniya, za a duba shi a asibitinka.

“Kwamitin Zartarwa na Anjuman e-Haideri, dake Jor Bagh, a New Delhi, ta Izinin Uban Ƙungiyarmu, Maulana Kalbe Jawad Naqvi, ya yanke shawarar ɗaukar nauyin dukkan kuɗaɗen magani da za a buƙata a nan Indiya don duba lafiyarsa.

“Muna fata za a duba buƙatarmu, a yi abinda ya dace”.

A cewar rahotanni, Mista El-Zakzaky yana fama da ciwon zuciya, matsanancin hawan jini, rashin gani da idonsa na dama da yake ci gaba, taɓuwar ƙwaƙwalwa da sauransu.

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan