Shahararren jarumin nan na Kannywood ɗin, Adam Zango ya tsira a wani haɗari mota yayinda yake dawowa daga Jamhoriyar Nijar.
Mista Zango ya je Niamey ne, babban birnin Nijar don yin wasan Bikin Babbar Salla.
Mista Zango ya bayyana a shafinsa na Instagram cewa haɗari ya haɗa da shi da wasu a bokansa.
Ya ƙara da cewa motar ce kaɗai ta samu matsala, amma dukkanisu sun tsira.
Da yawa daga cikin jaruman Kannywood sukan yi tafiye-tafiye lokacin bukukuwan Salla don yin wasa.
Turawa Abokai