Buhari ya sa ranar da zai rantsar da sabbin ministoci

182

Shugaba Muhammadu Buhari zai rantsar da sabbin ministoci ranar Laraba, 21 ga Agusta, a cewar Ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya.

Wata sanarwa daga Babban Sakataren Ofishin Kula da Ministoci, Babatunde Lawal, ta ce za a yi taron sanin makamar aiki da ministocin ranar 19 da 20 ga Agusta. Tun da farko, an shirya gudanar da taron sanin makamar aikin ne ranar 15 da 16 ga Agusta.

A ranar 2 ga Agusta, Sakataren Gwamnatin Tarayya, Boss Mustapa, ya gayyaci sabbin ministocin don su karɓi takardun da suka kamata don su yi nazari su kuma samu jagoranci, kafin rantsar da su.

Takardun sun haɗa da Rahoton Matsayin Manufofi, Shirye-shirye da Aikace-aikace, Jagorar Gudanar da Aiki daga 2019-2023, Littafin Majalisar Zartarwa ta Ƙasa, wato FEC Handbook, da sauransu.

Mista Boss ya kuma buƙace sabbin ministocin da su miƙa kwafin takardun shaidar gogewarsu ta aiki, wato CVs, da kuma kowace irin shaida.

Ana buƙatar su miƙa kwafin takardun na zahiri da kuma na Intanet.

A ranar 23 ga Yuli ne Shugaba Buhari ya naɗa ministoci 23 daga jihohin ƙasar nan 36, da Birnin Tarayya, Abuja.

Daga cikin sabbin ministocin akwai tsohon Gwamnan Jihar Akwa Ibom, Godswill Akpabio; Babban Lauya, Festus Keyamo; tsohon Gwamnan Jihar Benue, George Akume; da sauran mutane 40.

Shugaban Ƙasar ya dawo da Babatunde Fashola, Chris Ngige da wasu ‘yan kaɗan a matsayin ministoci.

An naɗa ministocin ne daga shiyyoyin siyasa shida na ƙasar nan.

Tuni Majalisar Dattijai ta tantance su.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan