Hukumar Tace Finafinai ta Jihar Kano ta hana masu shirya finafinai na Kannywood yin finafinai dake nuna kisan ma’aurata.
Babban Daraktan Hukumar, Isma’il Na’abba Afakallah ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba a Kano.
Sanarwar, wadda mai magana da yawun Hukumar, Ibrahim Adamu Ƙofar Na’isa ya sanya wa hannu, ta zargi masu shirya finafinai na Kannywood da shigo da sabon salo a masana’antar, dake nuna maza na kashe matansu, ko kuma mata na kashe mazajensu.
Mista Afakallah ya tunatar da masu shirya finafinai cewa manufar shirya finafinai shi ne a nuna kyawawan ɗabi’u na tarbiyya, al’ada, gargajiya da addini na al’umma.
Ya ƙara da cewa Hukumar ta kammala shirye-shiryen don fara tantance dukkan masu ruwa da tsaki dake Kannywood.