Home / Labarai / Sarki Sanusi ya buƙaci a sauke lemarsa yayinda ake tsaka da ruwan sama

Sarki Sanusi ya buƙaci a sauke lemarsa yayinda ake tsaka da ruwan sama

A ranar Alhamis ɗin nan ne ruwa ya daki Sarkin Kano, Muhammad Sanusi II yayinda yake gudanar da Hawan Ɗorayi, wanda ke nuna ƙarshen bukukuwa Salla a Kano.

Jaridar Kano Today ta ruwaito cewar Sarki Sanusi II ya umarci fadawa da su sauke lemar, saboda tsarin fada bai ba mahaya dawakai damar amfani da lema ba.

Sarkin ya fito ne ta Ƙofar Ƙwaru ya biyo ta Mandawari, Madungurum, Garangamawa, Warure, Aisami da Goron Dutse.

Tawagar Sarkin ta bar cikin birni suka bi ta Ƙofar Famfo, suka yada zango Gandun Sarki dake Ɗorayi, wanda aka fi sani da Gidan Mahaifiyar Sarki, a Ƙaramar Hukumar Gwale.

A daidai Ƙofar Famfo ne ruwan sama ya ɓarke.

Bisa al’ada dai, Sarkin Kano yakan yi Hawan Panisau ne a Babbar Salla, an maye gurbin sa ne da Hawan Daushe don kar a taka gonaki a yankin na Panisau

About Hassan Hamza

Check Also

Majalisar Dokokin Kwara Ta Yi Kira Da A Kwashe Almajirai A Jihar

Majalisar Kwara Na Yunƙurin Kwashe Almajirai Daga JiharMajalisar Dokokin Jihar Kwara ta yi kira ga …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *