An samu wata ‘yar dirama yau Juma’a a Filin Jirgin Saman Ƙasa da Ƙasa na Nnamdi Azikwe dake Abuja lokacin da jami’an tsaro na farin kaya, wato DSS suka dira suka kuma tafi da Jagoran Ƙungiyar Islamic Movement of Nigeria, IMN, Ibrahim El-Zakzaky, da matarsa, Zeenat, a cewar jaridar The Independent.
An kawo Mista El-Zakzaky ne da matarsa a Ethiopian Airline ET911 da misalin ƙarfe 11:50 na safiyar Juma’ar nan, biyo bayan ce-ce-ku-ce da aka samu bayan tafiyarsa asibiti a Indiya don duba lafiyarsa.
Jami’an na DSS sun fitar da shi ta sashin fitar Shugaban Ƙasa. An hana ‘yan jarida zuwa kusa da wajen da jirage ke sauka don ɗaukar yadda ya sauka.
An gano cewa jami’an tsaron sun tuƙo motar asibiti ne zuwa wajen da jirage ke sauka da kujerar ɗaukar mara lafiya, yana sauka daga jirgin sai suka yi maza suka ɗauke shi.
Jaridar The Independent ba ta tabbatar da inda aka kai shi ba har lokacin da aka rubuta wannan rahoto.