‘Yan sanda a jihar Legas sun samu nasarar kama wata mata da aka dauki hotonta tana cin zarafin wani yaro sannan ta kulle shi a wani keji na karnuka.
Babu tabbas kan lokacin da aka dauki bidiyon amma an rinka yada shi a shafukan Twitter a farkon watan nan.
Sai dai an ga matar a bidiyon, tana dukan yaron da bel.
Daga nan sai ta saka shi a wani keji ta rufe sannan ta kama gabanta.
Akwai wasu karnuka biyu a cikin wani keji kusa da wanda ta saka yaran.
Bidiyon ya tayar da hankulan mutane a shafukan sada zumunta, inda wasu suka yi alkawarin bayar da lada ga duk wanda ya taimaka aka gano inda matar take.
A ranar Alhamis, mai magana da yawun ‘yan sanda, Dolapo Badmos, ta wallafa a shafin Twitter cewa an kama matar.
Ta ce “Matar na hannun jami’an tsaro kuma za a gurfanar da ita a kotu… An kubutar da yaron, wanda maraya ne, kuma ana kula da shi a wani wurin mallakin gwamnatin Legas.”
Matar Da Kulle Yaro A Cikin Kejin Kare Ta Shiga Hannun Ƴan sanda
Turawa Abokai