Najeriya Za Ta Tarwatse Kuma Ƴan Arewa Ne Za Su Sha Wahala – In Ji Sheikh Gumi

150

Fitaccen Malamin addinin Musuluncin nan Dakta Ahmad Abubakar Mahmud Gumi, yayi gargadi akan cewar ƙasar nan na iya rabewa gida biyu kuma yankin arewa ne za su fi shan wahala.

Malamin ya ce rikici zai balle a arewa idan hakan ta faru yayin da yankin kudu za su yi kokari wajen daidaita yankunansu.

“Na ga matsala na tunkaro Najeriya, kuma hakan ba karamin illah zai yiwa ‘yan Najeriya ba,” Gumi ya bayyanawa jaridar Sun.

“Bari na fada muku abinda zai faru da yankin arewa idan har ƙasar nan ta rabe gida biyu.

Yankin kudu maso yamm da yankin kudu maso gabas za su yi ƙoƙarin ganin sun daidaita yankunansu, yayin da yankin arewa zai kasance cikin rikici da tashin hankali.

Daga yaya zamu iya kawo ƙarshen Boko Haram dake yankin arewa maso gabas? Daga yaya zamu kawo ƙarshen matsalar fulani makiyaya a arewa? Ba zamu iya kawo ƙarshensu ba.

“Maganar gaskiya ma shi ne, kokarin da yankin kudu su ke yi wajen yaƙarsu shi ne yake rage musu ƙarfi, amma idan suka tafi suka barmu da su na tabbata arewa ta gama lalacewa kenan.

“Kuma Najeriya za ta zama kamar ƙasar Lebanon ko Yemen. Babu wanda zai iya kawo ƙarshen matsalar arewa tunda babu wani wanda yake da wannan ƙarfin a arewa.

“Duk mutanen arewa kowa na nuna ɓangaranci na yare in da hakan ba ƙaramin barazana bace ga ƙasar nan. Yankin kudu maso yamma suma sun rarrabu amma kuma su basu kaimu rikici ba.

“Za su iya yarjejeniya wajen kawo ƙarshen matsalar dake tsakaninsu, saboda su abinda suka sani shine kasuwancinsu,” in ji shi

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan