Atiku ya buƙaci kotu ta bayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaɓen Shugaban Ƙasa

161

Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasar Najeriya, Atiku Abubakar da jam’iyyar PDP, su roƙi Kotun Sauraron Ƙorafe-ƙorafen Zaɓen Shugaban Ƙasa da ta bayyana su matsayin waɗanda suka yi nasara a zaɓen Shugaban Ƙasa da aka yi ranar 23 ga Fabrairu, 2019.

Mista Atiku da jam’iyyarsa sun bayyana wannan buƙata ne a jawabinsu na ƙarshe mai shafi 43 da suka miƙa wa Kotun Sauraron Ƙorafe-ƙorafen Zaɓen Shugaban Ƙasa ta hannun lauyansu, Livy Uzoukwu, ranar 14 ga Agusta.

Atiku da PDP, waɗanda su ne masu ƙara suka ce sun tabbatar da iƙirarinsu cewa Shugaba Muhammadu Buhari ba shi da mafi ƙarancin takardar shaidar karatu ta sakandire da ya kamata a ce ya yi takara da ita.

A cewarsu, saboda haka, ya kamata Kotun ta sauke Shugaba Buhari bisa waɗannan dalilai.

Dama dai ranar 1 ga Agusta, kotun ta ɗaga zamanta zuwa 21 ga watan na Agusta, a matsayin ranar da za ta saurari jawaban ƙarshe jim kaɗan bayan da waɗanda ake ƙara sun gama bada jawabinsu na kariya a kan ƙarar da Atiku da PDP suka shigar da su.

Da suke tabbatar da iƙirarinsu, masu ƙarar sun shigar da shaidu 62 da kuma takardu, haɗi da shaidun bidiyo.

Yayinda Shugaba Buhari, a matsayin wanda ake ƙara na biyu ya gabatar da shaidu bakwai kaɗai, daa kuma takardu kaɗan don kare nasararsa, Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa, INEC da APC sun ce za su dogara ne da shaidun da masu ƙara za su gabatar a lokacin bincikensu na ƙwaƙwaf.

Sai dai Mista Atiku da PDP a jawabin nasu na ƙarshe, sun roƙi kotun da ta soke zaɓen Shugaba Buhari tunda sun tabbatar da cewa bai cancanta ya yi takara a zaɓen ba.

Banda haka, sun ce tabbatar da dukkan zarge-zargen da suke a cikin ƙararsu game da yadda INEC ta gudanar da zaɓen.

A cewar su, manya-manyan abubuwa biyar da ya kamata kotun da Mohammed Garba ke jagoranta ta lura da sun haɗa da ko Buhari ya cancanta ya yi takara a zaɓen.

“Ko Buhari ya miƙa wa INEC takardar rantsuwar kotu dake ƙunshe da bayanan ƙarya ƙarara don taimaka masa ya cancanci yin takara a zaɓen da ake magana.

“Ko an tabbatar daga ƙara da shaidu cewa an zaɓi Buhari ne ta hanyar mafiya rinjayen sahihan ƙuri’u da aka kaɗa a zaɓen.

“Ko zaɓen Shugaban Ƙasa da INEC ta gudanar ranar 23 ga Fabrairu ba shi da inganci saboda aikace-aikacen cin hanci.

“Ko zaɓen Shugaban Ƙasa da INEC ta gudanar ranar 23 ga Fabrairu ba shi da sahihanci saboda dalilin ƙin bin Dokar Zaɓe ta 2010 da aka yi wa kwaskwarima, Tsare-tsaren Zaɓen 2019 da kuma takardun da aka bayar don gudanar da zaɓen”, suka faɗi haka a kundin ƙarar da PREMIUM TIMES ta gani ranar Juma’a.

Masu shigar da ƙarar sun ce hatta shaidun da Mista Buhari ya gabatar don su kare shi, da aka yi binciken ƙwaƙwaf, sun tabbatar da gaskiyar cewa Shugaban Ƙasar ba shi da takardar shaidar kammala sakandire, a matsayin mafi ƙarancin abinda za a iya yin takarar ofishin Shugaban Ƙasa da ita.

“Saboda haka, mun miƙa dukkan ƙirƙirarrun hujjoji da wanda ake ƙara na biyu (Buhari) ya jagoranci gabatarwa don ya tabbatar da cewa ya halarci sakandire ko firamare ko kuma cewa ya halarci wasu kwasa-kwasai ba su da inganci saboda bai dogara da ko ɗaya daga cikin waɗannan takardu ba a hujjar exhibit P1, ya dogara ne da takardar shaidar kammala firamare, shaidar WASC da Officer Cadet.

“Haka kuma yunƙurinsa na kafa hujjar cewa zai iya magana da rubutu da yaren Turanci ya tashi a banza. Dukkan waɗannan ba su da muhimmanci saboda gazawarsa na kawo takardarsa ta kammala firamare, takardar shaidar kammala sakandire ko WASC, da shaidarsa ta Officer Cadet, ko ma dai me wannan yake nufi. Officer Cadet ba ba takardar shaidar karatu ba ce a ƙarƙashin tsarin mulki da Dokar Zaɓe; ba a santa a wata doka ba”, in ji su.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan