Dubban ɗalibai ne suka rubuta Jarrabawar Tantancewa ta BUK

172

Jimillar ɗalibai 12,209 ne suka zauna Jarrabawar Tantancewa ta Jami’ar Bayero ta Kano ta Shekarar 2019, a cewar Mataimakin Jami’ar Mai Kula da Harkokin Karatu, Farfesa Adamu Idris Tanko.

Farfesa Tanko ya ce ɗalibai 15,817 ne suka nemi gurbin karatu a BUK a shekarar karatu ta 2019/2020, daga ciki, ɗalibai 12,209 suka zana Jarrabawar Tantancewar.

Mataimakin Shugaban Jami’ar ya bayyana gamsuwarsa bisa yadda aka gudanar da jarrabawar gaba ɗaya, ya ce tantancewar ta gudana yadda ya kamata, kuma jami’ai sun kula da aikinsu sosai.

Ya ƙara da cewa an fara Jarrabawar Tantancewar kamar yadda aka tsara ba tare da wani tasgaro ba, kuma ba a samu rahoton maguɗin jarrabawa ba.

Magatakardar BUK, Fatima Mohammed, ita ma ta bayyana farin ciki bisa yadda aka tsara aka kuma gudanar da jarrabawar.

Ta bayyana cewa an samar da wurare da yawa don a rage cunkoson ɗalibai, yayinda aka samar da ɗakunan ko-ta-kwana guda biyu a tsohon matsugunin jami’ar da sabo don kar a bar aikin a waje ɗaya.

Miss Fatima ta yi nuni da cewa Jami’ar ta ɗauki ma’aikata malamai da waɗanda ba malamai ba waɗanda suka yi aiki a matsayin masu duba jarrabawa, da kuma wasu ɗalibai da suka yi aiki a matsayin ‘masu yi wa ɗalibai jagora’ wato ‘campus guide’ don tabbatar da gudanar aikin yadda ya dace.

Shi ma da yake tofa albarkacin bakinsa, Daraktan Cibiyar Fasahar Yaɗa Labarai, CIT, Farfesa Mohammed Ajiya, ya ce za a iya bayyana jarrabawar a matsayin nasara sosai, saboda ba ta wahalar ba.

Ya ce an gudanar da aikin tantancewar ne a lokuta biyu, an ba ɗaliban safe da na rana lokutan yin jarrabawar daidai da kwasa-kwasansu.

Ya ce an ba kowane ɗalibi tambayoyi ne daidai da kwasa-kwasan da ya yi rijista da su a Hukumar Shirya Jarrabawar Shiga Manyan Makarantu, JAMB, kuma tambayoyin kowa an yi masa tasa, kuma an hargitsa su don kauce wa maguɗin jarrabawa.

Ita ma, Shugabar Sashin Jarrabawa, Guraben Karatu da Adana Bayanai, DEAR, Amina Umar, wadda ta lura da yadda aka gudanar da tantancewar, ta bayyana cewa da yawa daga cikin ɗaliban sun nuna halin ɗa’a, sun kuma yi shigar da ta dace, tana mai lura da cewa ba a samu rahotonnin sojan-gona ba.

Wasu ɗalibai da suka rubuta jarrabawar, Ummuhani Ize (B.Sc Biochemistry) da Abubakar Ayuba (Ba.Sc Architecture) sun bayyana gamsuwa da irin tsarin da Jami’ar ta yi.

Shugaban Jami’ar, Farfesa Muhammad Yahuza Bello, wanda ya zagaya wuraren da aka gudanar da tantancewar, shi ma ya gamsu da yadda tsarin ya gudana.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan