Akwai yiwuwar a gurfanar da tsohon Gwamnan Kwara da muƙarrabansa a kotu

91

Ta yiwu a maka tsohon Gwamnan Jihar Kwara, Abdulfatah Ahmed da waɗanda su ka yi aiki a gwamnatinsa a gaban kotu bisa rawar da ake zargin sun taka wajen yin wadaƙa da kuɗaɗen Gwamnati Jihar.

Waɗanda aka nuna wa yatsa aka kuma bada shawarar a gurfanar da su a gaban kotu a rahoton da kwamiti mai mambobi 21 da Gwamnan Abdulrahman Abdulrazaq ya kafa bisa zargin siyar da kadarorin gwamnati a lokacin gwamnatin tsohon gwamnan sun haɗa da tsohon Sakataren Gwamnatin Jihar a shekaru takwas na Mista Ahmed, Alhaji Isiaka Gold, Shugabanni Ma’aikatansa su biyu, Alhaji Ladi Hassan da Alhaji Baba Abdulwahab, Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kwara ta 7, Razak Antuwa da wasu da dama.

Majiyoyi da ke da kusanci da Gwamnatin Jihar Kwara sun ce an samu da yawa daga cikin tsaffin jami’an gwamnatin da hannu cikin cefanar da gidajen gwamnati na GRA a Ilorin, waɗanda sun kusa 100, waɗanda Majalisar Dokokin Jihar ta yi amfani da su, da filayen mallakar Gwamnatin Jihar da ke jihohin Legas da Kaduna, da Babban Birnin Tarayya, Abuja.

Majiyoyin su ka ce an siyar da mafi yawa daga cikin gidajen da filayen dake wurare daban-daban ga waɗanda su ka yi aiki a gwamnatin ko abokansu a farashi mai rahusa yayinda aka siyar da gidajen dake unguwar ‘yan majalisa ga ‘yan majalisu da su ka yi aiki a Majalisar Dokokin Jihar ta Bakwai daga 2011 zuwa 2015.

A cewar jaridar THE PUNCH, a ranar Juma’a Gwamna Abdulrazaq ya ce ta yiwu gwamnati ta garzaya kotu don ƙwato kadarorin da gwamnatin da ta gabata ta siyar ba bisa ka’ida ba.

Lokacin da ya ke karɓar rahoton ƙarshe na kwamitin da ya duba yadda gwamnatin baya ta siyar da kadarorin gwamnati, Gwamnan Abdulrazaq ya ce zai yi amfani da shawarwarin kwamitin a kotu don ƙoƙarin yi wa al’umma adalci.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan