Kungiyar Kwallon Kwando Ta Mata Ta Najeriya Tazamo Zakara

26

Kungiyar kwallon kwando ta mata ta Najeriya wato D’Tigress ta zamo zakara a gasar cin kofin kwallon kwando ta Afrika ta mata da aka kammala a daren yau a birnin Dakar na kasar Senegal.

D’Tigress din ta zamo zakara ne bayan ta lallasa masu masaukin baki wato Senegal inda tun daga kashin farko zuwa kashi na 3 na wasan Najeriya ce take jan ragamar amma azagaye na 4 na karshe wasa ya kasancewa Najeriya inda sukaji jiki suka sha da kyar daci 60 da 55.

Haka shekaru biyu da suka gabata wato 2017 Najeriya ce ta zamo zakara a gasar ta Afrika.

Za a iya cewa dai kungiyar kwallon kwando ta mata ta Najeriya wato D’Tigress tazamo gagarabadau a nahiyar Afrika ganin yadda take cin karenta babu babbaka.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan