Cp Ahmed Iliyasu Agogo Sarkin Aiki Ne – In ji Wakilin Ƴan Chana A Kano

171


Wakilin mazauna ƙasar China a jihar Kano ya Bayyana kwamishinan ƴan sandan jihar Kano a matsayin agogo sarkin aiki.

Tun day farko wakilin China din ya bayyana hakan a lokacin da ya kaiwa kwamishinan ƴan sandan ziyarar girmamawa a ofis din sa da ke yankin unguwar Bompai a birnin Kano

A lokacin ziyarar ya yabawa irin kokarin da rundunar ƴan sanda ta ƙasa reshen jihar Kano su ke yi, tare da ƙarfafa musu gwiwa akan cigaba da aiyukansu.

A nasa ɓangaren kwamishina Ahmed Iliyasu ya bayyana jin dadinsa dangane da wannan ziyarar da wakilin ƴan Chana ya kai masa, ya kuma tabbatar da cewa wannan ziyarar ita ce matakin da za ta ƙarfafa dangantaka tsakanin ƴan ƙasar China mazauna Kano da rundunar ƴan sanda.


Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan