NASU, SSANU Reshen BUK sun tsunduma yajin aiki

164

A ranar Litinin ɗin nan ne Ƙungiyar Ma’aikatan Da Ba Malmai Ba, NASU, da Ƙungiyar Manyan Ma’aikatan Jami’o’i, SSANU, Reshen Jami’ar Bayero ta Kano, BUK suka bi sahun takwarorinsu na sauran jami’o’i wajen shiga yajin aikin gargaɗi na ƙasa gaba ɗaya na tsawon mako ɗaya bisa gazawar gwamnati na cika musu alƙawarin da ta yi musu.

Rahotonni sun ce Kwamitin Haɗin Gwiwa na SSANU da NASU ya ba Gwamnatin Tarayya wa’adin kwanaki 14 don ta warware musu matsalolinsu, wa’adin kuma ya ƙare ranar Lahadi ba tare da an cika musu alƙawarin ba.

Haruna Aliyu, Shugaban SSANU, Reshen Jami’ar Bayero ta Kano, ya sanar da matakin tafiya yajin aikin biyo bayan wani taron tattaunawa da ƙungiyar ta yi ranar Litinin.

“Yajin aikin na gaba ɗaya ne, kuma ya game ko’ina, tunda an umarci dukkan mambobinmu da su yi biyayya, hatta asibit ma ba a ƙyale ba”, in ji Mista Aliyu.

Mista Aliyu ya ce maƙasudin yajin aikin shi ne nuna rashin jin daɗi bisa yadda gwamnati ta nuna son kai wajen biyan alawus-alawus ga ma’aikatan jami’o’i, inda ta ware kaso 20 cikin ɗari kawai ga ma’aikatan da ba malamai ba, yayinda malamai suka karɓi kaso 80 cikin ɗari daga cikin Biliyan 25 da aka saki.

A cewar Shugaban Ƙungiyar, wani dalilin kuma shi ne ƙin dawo da mambobin SSANU bakin aiki da Gwamnatin Tarayya ta yi, duk da hukuncin da wata Kotun Ma’aikata ta bayar tun 2016.

Ya ƙara da cewa Gwamnatin Tarayya ta kuma ƙi ta sake tattauna yarjejeniyar 2009 da ma’aikatan da ba malaman ba, duk da amincewa da yin hakan da ta yi.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan