Wani Magidanci A Katsina Ya Yiwa Iyalinsa Wanka Da Ruwan Guba

118

Wani mutum mazaunin jihar Katsina ya watsawa matarsa da ƴaƴansa guda biyu ruwan guba a lokacin da su ke tsaka da sharar barci.
Wannan al’amari ya faru a yankin ƙaramar hukumar Dandume da ke jihar ta Katsina.

Tun da farko dai wasu rahotanni sun bayyana cewa wannan magidanci ma’aikacin bankin union ne reshen ƙaramar hukumar Funtua. Rahotannin sun ƙara da cewa bayan ya aikata wannan ɗanyen aiki ne ya cika wandonsa da iska.
Tuni dai aka garzaya da mai dakin nasa tare da sauran ƴaƴansa guda biyu zuwa asibitin koyarwa na jami’ar Ahmadu Bello da ke Shika domin neman magani.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan