Wasu Matasa Masu Yi wa Ƙasa Hidima sun rasu a Katsina sakamakon haɗarin mota

183

Hukumar Kula Matsa Masu Yi wa Ƙasa Hidima, NYSC ta Jihar Katsina ta tabbatar da mutuwar Matasa Masu Yi wa Ƙasa Hidima su uku a wani mummunan haɗarin mota a Ƙaramar Hukumar Ƙanƙara dake jihar.

Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da Jami’in Huɗda da Jama’a na Hukumar, Alex Obemeata ya bayar ranar Lahadi a Katsina.

“Lahadi, 18 ga Agusta, 2019, rana ce ta baƙin ciki a ga NYSC a Katsina saboda Matasa Masu Yi wa Ƙasa Hidima su uku sun rasa rayukansu a wani mummunan haɗarin mota a kan hanyarsu ta zuwa wata coci a Funtuwa.

“Matasan Masu Yi wa Ƙasa Hidima, waɗanda sun kai 12, suna cikin wata bas ne mallakin Ƙungiyar Matasa ‘Yan Katolika Masu Yi wa Ƙasa Hidima, Reshen Jihar Katsina.

“Nan take uku daga cikinsu suka mutu”, in ji Mista Obemeata.

“Jami’in Huɗɗa da Jama’ar ya ƙara da cewa haɗarin ya afku daidai lokacin da Gwamnan Jihar Katsina, Aminu Masari ke wucewa ta ƙauyen Gobirawa dake Ƙaramar Hukumar Ƙanƙara ranar Lahadi.

Ya ce Gwamnan ya tsaya, ya kuma bada umarnin a ɗauki wata mota a cikin tawagar mitocinsa don a kai waɗanda suka samu raunuka Babban Asibitin Jihar don samu kulawar likita.

Tuni an kai gawarwakin mutuware.

Ya bayyana cewa Shugaban NYSC na Jihar Katsina, Alhaji Ahidjo Yahaya ya je asibitin bisa rakiyar wasu manyan ma’aikata, lokacin da motar asibiti dake ɗauke da waɗanda suka samu raunuka da gawarwakin ta isa asibitin.

Koda yake Jami’in Huɗɗa da Jama’ar bai bayyana sunayen waɗanda suka rasa rayukan nasu ba, ya ce Mista Yahaya ya yi addu’ar Allah Ya ji ƙan su, Ya kuma ba iyalansu haƙurin jure rashin.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan