Yadda Mazauna Ƙaramar Hukumar Dala Ke Zaune Cikin Fargaba

161

Duk da irin ikirarin da gwamnatoci a faɗin ƙasar nan su ke akan samar da Ingantattun hanyoyi tare da magudanan ruwa a jihohinsu, domin magance matsalar ambaliyar ruwa.

Sai ga shi al’ummar unguwannin Gwammaja da Kofar Ruwa a yankin ƙaramar hukumar Dala a jihar Kano na cikin fargaba a duk lokacin da aka samu tasowar hadari, sakamakon rashin isassun mugudanan ruwa a wannan yanki.


Tun da farko dai ana samun ambaliyar ruwa akan titin da ya tashi daga kofar ruwa zuwa kan titin Katsina, in da ruwan ya kan kawo ababen hawa tare da matafiya a ƙasa cikas.

Mazauna waɗannan unguwanni sun bayyana takaicinsu akan yadda wannan matsala ta ƙi-ta-ƙi-cinyewa, tare da yin kira ga Gwamnan Jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje da ya kai musu ɗauki akan wanna matsala.


Mun yi ƙokarin ta bakin jin ma’aikatar aiyuka da gidaje ta jihar Kano, sai dai kawo wannan rahoto babban sakare a ma’aikatar yana halartar wata tattaunawa da ma’aikatansa

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan