Diezani Ta Buƙaci A Dawo Mata Da Sarƙokin Gwal Mallakinta

166

Tsohuwar ministar albarkatun mai Diezani Alison-Madueke, ta roƙi kotu da ta ba wa hukumar EFCC umarnin dawo mata da sarkokin ta na gwal da hukumar ta ƙwace daga gareta.
Diezani ta bayyana wannan bukata ne a wata ƙara da ta shigar ta hannun lauyanta Farfesa Awa Kalu a babbar kotun tarayya da ke birnin Legas.

Ta ƙara da cewa hukumar EFCC ta ci zarafin ‘yancinta na mallakar kayayyaki da amfani da su yadda ranta ke so, wanda kundin tsarin mulkin ƙasar nan sashe na 43 ya tanada.

Idan za’a iya tunawa dai tun a ranar 5 ga wata Yulin shekarar 2019 ne jami’an hukumar ta EFCC su ka kai same gidan tsohuwar ministar, in da su ka kwaso sarkoki da ‘yan kunne da zobba da wayoyi masu tsada ƙrar iPhone na gwal har guda 2,149, waɗanda kimarsu ta kai dala miliyan 40, kimanin naira biliyan 14.4.


Hukumar ta shaida wa kotu cewa lallai ta ga wadannan sarkoki tare da wayoyin iPhone ƙirar gwal a gidan tsohuwar ministar, kuma ta ɗebo su, saboda hankali ya nuna cewa ministar ta same su ne ta ɓarauniyar hanya. Kuma tana fata kotu ta damkawa gwamnati su su zama mallakinta.


A ƙarshe Diezani ta roƙi kotu ta ƙi amincewa da buƙatar hukumar, na ƙwace mata gwalagwalanta tare da dawo mata da ababenta.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan