Gwamnan Ekiti ya hana amfani da Turanci a tarukan gargajiya a jihar

68

Gwamna Kayode Fayemi na Jihar Ekiti ya hana amfani da harshen Turanci a matsayin hanyar sadarwa a yayin tarukan gargajiya a kowane ɓangare na jihar.

Gwamnan, wanda ya bada umarnin ranar Litinin a Ado-Ekiti a yayin Taron Nuna Al’adu na Masu Ruwa da Tsaki na Jihar Ekiti Irinsa na Farko, ya ce daga yanzu ya zama laifi ga wani ya yi magana da Turanci yayin tarukan gargajiya.

Mista Fayemi ya ce gwamnatinsa tana son a ciyar da fasaha da al’ada a jihar gaba ta hanyar kari irin na Yarbanci da na Ekiti, yana mai cewa wannan zai mayar da abin wajibi a wannan lokaci.

Mista Fayemi, wanda ya samu wakilcin Shugaban Ma’aikata, Deji Ajayi, ya bayyana cewa jihar za ta yi Taron Nuna Hikimomi da Nuna Al’adu a watan Disamban bana a matsayin wani ɓangare na bunƙasa tattalin arziƙi.

“Daga yanzu, gwamnati ta hana magana da Turanci a duk wani taron gargajiya. Duk wanda zai yi taro dole ya yi maganan da Yarbanci ko kafin harshenmu”, in ji Mista Ajayi.

Turawa Abokai

1 Sako

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan