Na Yafewa Waɗanda Su Ka Kai Min Hari A Jamus – In Ji Sanata Ekweremadu

121

Tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawan ƙasar nan sanata Ike Ekweremadu ya bayyanawa cewa ya yafewa waɗanda su ka kai masa hari a ƙasar Jamus.

Sanata Ekwemeradu ya bayyanawa manema labarai hakan ne jim kaɗan da saukarsa a filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe da ke birnin tarayya Abuja, in da ya ƙara da cewa waɗanda su ka kai masa harin mashaya be.

“Ina da yaƙinin cewa suna cikin mayen giya tare da miyagun ƙwayoyi. Kuma ba sa wakiltar buƙataun a’lummarmu. Saboda haka na yafe musu domin ba sa gabana” in ji sanata Ekwemeradu

Ya ƙara da cewa gwamnatin ƙasar jamus ce ta ke da alhakin ɗaukar dukkanin wani mataki da ya dace akan waɗanda su ka kai masa harin.

Sanatan Ekweremadu ya ce waɗanda su kai masa harin sun buƙaci da ya yi musu ƙarin bayani akan rawar da ya taka a lokacin da gwamnatin tarayya ta ƙaddamar da sumamen nan mai taken rawar mesa a yankin kudu maso gabashin ƙasar nan, da nufin kawo ƙarshen masu zangar-zangar neman ƴancin ƙasar biyafara.


Bayan na fara jawabin gaisuwa a garesu, sai su ka fara yi min ƙorafi tare da zargin muna da hannun akan wannan sumame. In da ɗaya daga cikinsu ya fara nuna ni akan ina da hannu a cikin lamarin.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan