Yadda Wani Farfesa Ya Ɗirkawa Dalibarsa Mai Shekaru 16 Ciki A Jihar Ekiti

367

ASHAFA MURNAI

Asirin wani farfesa kuma tsohon shugaban sashen nazarin aikata alifuka a Jami’ar Gwamnatin Tarayya ta Jihar Ekiti ya fito fili, bayan kama shi da aka yi da laifin dirka wa dalibar da mai shekaru 16 cikin shege.

Farfesa Adewole Atere, ya yi wa dalibar sa mai suna Precious Azuka cikin shege a lokacin da ta zo jami’ar a shekarar karatun ta ta farko.

Ta fara haduwa da shi a cikin watan Maris, 2017, a lokacin ta na da shekaru 16 da haihuwa. An tabbatar da cewa daya daga cikin malaman sashen ne, ne mai suna Dakta Chinedu Abrifor ne Atere ya tura wurin karamar yarinyar, ya isar da sakon soyayyar sa a gare ta.

PREMIUM TIMES ta zakulo wasu shaidu na maganganun da aka yi rikodin da ke tabbatar da cewa Mista Abrifor ya shaida wa Azuka cewa ‘ai ta kai munzilin kwanciya tare da Mista Atere.’

A lokacin da Azuka ta bayyana a gaban Kwamitin Bincike, ta bayyana cewa:

“Kwanaki kadan bayan Mr. Abrifor ya ce min na kai munzilin fara kwanciya da Mista Atere, sai ya rako shi har gidan kwanan mu na dalibai. Suka dauke ni zuwa gidan sa da ke Aiyegbaju, inda na kwana tare da shi a can.

“Sai washegari karfe 6 na safe ya maida ni gidan kwanan mu na dalibai. Daga nan sai ya rika dauka ta zuwa gidan sa ya na kwana da ni har tsawon makonni da dama.”

A gefe daya kuma, yayin da saurayin Azuka mai suna Kayode Fasanya ya gano cewa ta na soyayya da Farfesa Atere, sai ya rabu da ita, ya kama gaban sa. Azuka da Fasanya sun fara soyayya tun cikin Janairu, 2017.

YADDA ASIRIN FARFESA ATERE YA TONU

Watanni biyu bayan fara soyayya da Farfesa da kuma yarinya Azuka, sai Azuka ta fahimci cewa ta na fama da rashin lafiya. Awon da aka yi mata a asibiti ya tabbatar da cewa ta na da ciki.

“Da farko na yi kokarin zubar da cikin, amma sai likitan da ya yi min awon cikin ya min shi ba ya zubar da ciki.

“Daga nan sai na sha ganyen shayin Lipton da lemon tsami. Wannan kuwa ya haifar min da zubar da jini mai yawa.

“Da nag a na yi fashin al’ada ta wata na gaba, sai ban damu ba. A tunani na jinin da na zubar cikin ya fita kenan.”

Duk wannan bayani Azuka ce ta yi wa Kwamitin Bincike ana rekodin.

Yayin da aka shiga watan Yuli, sai kamannun Azuka sukacfara canjawa, inda hakan ke nuna cewa ta dauki ciki kenan. Haka nan a cikin gidan kwanan su na dalibai da kewaye, duk aka rika gulmar cewa Azuka ta dauki cikin shege.

YADDA AKA ZUBAR DA CIKIN AZUKA

Ta shaida wa kwamiti cewa wata kawar ta ce mai suna Priscilla ta kai ta wani dakin gwaji a Asibitin Oye Ekiti, inda wani mai suna Dakta Dada ya zubar mata da cikin a ranar 27 Ga Yuli. Amma fa a lokacin har cikin ya fara zama zama dan-tayi.

YADDA ASIRI YA TONU

To wasu masu shara na cikin tattara kwandunan zuba shara a gidan kwanan su Azuka na dalibai, sai suka ga wata jakar leda daure, amma kuma jini na diga daga cikin ta. Sai wannan mai shara ta kira abokan aikin ta masu shara ta nuna musu. Kuma suka nemi sanin daga ina ne aka jefar da ledar.

Ranar Alhamis ce da safe, kuma yawancin daliban duk ba su cikin gidan, sun fita zuwa ajujuwan su. To hakan ya sa ba su sha wahalar gano dakin da ya rage wata ke ciki ba ta fita ba.

Masu sharar nan sun samu Azuka kwance a galabaice, saboda ta zubar da jini mai yawan gaske, da kyar ma ta ke iya magana. Haka dai wata majiya ta shaida wa PREMIUM TIMES a cikin jami’ar, kuma ta ce a sakaya sunan ta.

Daga nan ne aka gaggauta kai Azuka Asibitin cikin jami’ar, aka kwantar da ita, amma washegari ranar 28 Ga Yuli aka sallame ta. Daga nan ne kuma hukumar makaranta ta kafa kwamitin bincike.

AN KAFA KWAMITIN BINCIKE

Wani lauya ne dan rakadi mai suna Olauli Ayodele, mazaunin Ado-Ekiti, ya rubuta wa hukumar jami’ar wasika. Daga nan jami’ar ta kafa kwamitin bincike a ranar 10 Ga Agusta, 2017.

AN BANKADO ATERE, LALATACCEN LAKCARA

Kwamitin bincike ya mika rahoton cewa:

“Bayan an sallami Azuka daga asibiti a ranar 28 Ga Yuli, 2017. Sai Dakta Abrifor ya kira ta, kuma ya kira tsohon saurayin ta Fasanya, domin su yi ganawar sirri a karamar harabar jami’ar da karfe 6 na yammacin ranar 2 Ga Agusta, 2017. Daga nan kuma suka nausa Ifaki Ekiti domin sake yin wata ganawar a can.

“A wurin ganawar sirrin dai Dakta Abrifor ya zargi Fasanya da dirka wa Azuka ciki. Shi kuma ya hau shi da hayaniya. Daga nan sai Abrifor ya dauki waya ya kira matar sa, ya ce ta lissafa masa kwanukan shigar ciki daga watan Maris zuwa Yuli. Matar sa ta ce masa tsakanin makonni 21 ko 22 kenan. Wato daidai ranakun da sakamakon gwajin da aka yi wa Azuka ya nuna.

Wannan ya sa malamin ya bai wa Fasanya, wato tsohon saurayin Azuka hakuri, amma kuma ya roke shi cewa ya daure ya karbi cikin ya ce shi ya yi, domin a rufa wa Farfesa Atere asiri.

“Sannan kuma ya ce idan Fasanya, wanda shi ma dalibi ne a makarantar ya amince zai karbi cikin, to za a biya dukkan kudaden da Azuka ta kashe, kuma za a ba shi kudade tare da maki mai daraja ta daya a jarabawar sa. “

PREMIUM TIMES ta gano cewa Fasanya tsohon saurayin Azuka ya ki karbar alhakin dirka wa Azuka ciki da kuma alhakin zubar mata da ciki, tunda ba shi ne ya yi mata ba. Shi kuma Farfesa Atere ya ajiye aikin sa.

A waje daya kuma an zargi shugaban jami’ar da kokarin binne maganar, kafin daga bisani aka hura masa wuta.

Amma dai yanzu haka Farfesa Atere ya samu wani aikin koyarwa a Jami’ar Olabisi Onabanjo, OOU, da ke Ago-Iwoye, Jihar Ogun.

PREMIUM TIMES ta nemi jin ta bakin Shugaban Jami’ar Tarayya ta Ekiti, wanda ya ce sun ki hukunta Farfesa Atere ne saboda lokacin da abin ya taso ya rigaya ya yi murabus, ya ajiye aikin sa.

Ya ce tunda ya ajiye aiki kuwa, jami’ar ba ta da hurumin hukuncta shi kenan.

Da aka tambayi Atere ta wayar tarho, ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa sharri ne aka yi masa, bai dirka wa Azuka ciki ba.

A yanzu dai Azuka ta na aji na ‘300 Level’ ne. Kenan har yanzu ta na jami’ar ba ta bari ba.

Har ila yau, PREMIUM TIMES ta kira lambar wayar Dr. Dada da Priscilla ta raka Azuka ya zubar mata da ciki. Sai ya kare kan sa ya ce ba shi ba ne, kuma asibitin su ba a zubar da ciki.

Sai dai kuma kamar yadda Atere ya kashe waya bayan ya ce sharri aka yi masa, bai kara yin wani bayani ba. Shi ma Dada bai kara cewa komai ba.

Sai dai kuma abin tambaya a nan, ko abin da ya faru tsakanin Farfesa Atere da Azuka na faruwa a sauran jami’o’i da sauran makarantun gaba da sakandare na kasar nan. Wanda ya sani to ya sani. Wanda bai sani ba, ba zai kar-da komai ba.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan