A ranar Larabar nan ne Shugaba Muhammadu Buhari ya rantsar da sabbin ministocinsa tare da ba kowane ɗaya daga cikin su ma’aikatar da zai riƙe tsawon shekaru huɗu.
An yi Bikin Rantsuwar ne a Fadar Shugaban Ƙasa dake Abuja.
Ga sunayen ministocin da muƙamansu, kamar yadda majiyarmu ta tabbatar mana.
1- Uchechukwu Ogah (Abia) – Ministan Ma’aikatar Tama da Ƙarafa
2- Muhammad Musa Bello (Adamawa) – Ministan Abuja
3- Godswill Akpabio (Akwa Ibom) – Ministan Neja Delta
4- Chris Ngige (Anambra) – Ministan Ƙwadago
5- Sharon Ikeazor (Anambra) – Ƙaramar Ministar Muhalli
6- Adamu Adamu (Bauchi) – Ministan Ilimi
7- Mariam Katagum (Bauchi) – Ministar Masana’antu, Kasuwanci da Zuba Jari
8- Timipre Sylva (Bayelsa) – Ƙaramin Ministan Man Fetur
9- George Akume (Benue) – Ministan Ayyuka Na Musamman da Harkokin Ƙasashen Waje
10- Mustapha Baba Shehuri (Borno) – Ƙaramin Ministan Noma da Raya Karkara
11- Goddy Jedi Agba (Cross River) – Ƙaramin Ministan Lantarki
12- Festus Keyamo (Delta) – Ƙaramin Ministan Neja Delta
13- Ogbonnaya Onu (Ebonyi) – Ministan Kimiyya da Fasaha
14- Osagie Ehanire (Edo) – Ministan Lafiya
15- Clement Anade Agba (Edo) – Ƙaramin Ministan Kasafin Kuɗi da Tsare-tsare
16- Otunba Richard Adeniyi Adebayo (Ekiti) – Ministan Masana’antu da Zuba Jari
17- Geofery Onyeama (Enugu) – Ministan Harkokin Ƙasashen Waje
18- Ali Isa Ibrahim Pantami (Gombe) – Ministan Sadarwa
19- Emeka Nwajiuba (Imo) – Ƙaramin Ministan Ilimi
20- Suleiman Adamu (Jigawa) – Ministan Albarkatun Ruwa
21- Zainab Shamsuna Ahmed (Kaduna) – Ministar Kuɗi
22- Mohammed Mahmoud (Kaduna) – Ministan Muhalli
23- Sabo Nanono (Kano) – Ministan Harkokin Noma
24- Bashir Magashi (Kano) – Ministan Tsaro
25- Hadi Sirika (Katsina) – Ministan Sufurin Jiragen Sama
26- Abubakar Malami (Kebbi) – Ministan Shari’a
27- Ramatu Tijani (Kogi) – Ƙaramar Ministar Abuja
28- Lai Mohammed (Kwara) – Ministan Yaɗa Labarai da Al’adu
29- Gbemisola Saraki (Kwara) – Ƙaramar Ministar Sufuri
30- Babatunde Raji Fashola (Lagos) – Ministan Ayyuka da Gidaje
31- Adeleke Mamora (Lagos) – Ƙaramin Ministan Lafiya
32- Mohammed H. Abdullahi (Nasarawa) – Ƙaramin Ministan Kimiyya da Fasaha
33- Zubairu Dada (Niger) – Ƙaramin Ministan Harkokin Ƙasashen Waje
34- Olamilekan Adegbiti (Ogun) – Ministan Ma’adanai da Ƙarafa
35- Tayo Alasoadura (Ondo) – Ƙaramin Ministan Ƙwadago
36- Rauf Aregbesola (Osun) – Ministan Harkokin Cikin Gida
37- Sunday Dare (Oyo) – Ministan Matasa da Wasanni
38- Pauline Tallen (Plateau) – Ministar Harkokin Mata
39- Rotimi Amaechi (Rivers) – Ministan Sufuri
40- Mohammed Maigari Dangadi (Sokoto) – Ministan Harkokin ‘Yan Sanda
41- Saleh Mamman (Taraba) – Ministan Lantarki
42- Abubakar B. Aliyu (Yobe) – Ƙaramin Ministan Ayyuka da Gidaje
43- Sadiya Umar Faruk (Zamfara) – Ministar Jin-ƙai da Walwalar ‘Yan Ƙasa