NITDA ta samu sabon shugaba

156

Shugaba Muhammadu Buhari ya naɗa Kashifu Inuwa Abdullahi a matsayin Darakta Janar kuma Babban Jami’in Zartarwa na Hukumar Bunkasa Fasahar Yaɗa Labarai ta Ƙasa, NITDA.

Garba Shehu, mai ba Shugaba Buhari shawara kan kafafen watsa labarai shi ya sanar da yin naɗin.

A cewar sanarwar, Shugaban ya kuma amince da maye gurbin waɗansu shugabannin Hukumomin Gwamnatin Tarayya da aka naɗa su ministoci kwanan nan.

Wasu daga cikin su sun haɗa da Basheer Garba Mohammed da ya maye gurbin Sadiya Umar Farouk a matsayin Kwamishinan Ƙasa na Hukumar Kula da ‘Yan Gudun Hijira, Baƙin Haure da Waɗanda Rikici Ya Raba da Muhallinsu.

An naɗa Dakta Chioma Ejikme a matsayin Babban Sakataren Hukumar Tsara Bayar da Fansho, ya maye gurbin Sharon O. Ikeazor.

Shuganan ya miƙa sunan Adeleke Moronfolu Adewolu ga Majalisar Dattijai don tabbatarwa a matsayin Babban Kwamishina (Masu Ruwa da Tsaki) a Hukumar Kula da Kamfanonin Sadarwa ta Ƙasa, NCC, wanda zai maye gurbin Sunday Akin Dare.

A cewar Mista Shehu, naɗe-naɗen sun fara aiki ne nan take.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan