Rukunin farko na alhazan Kano sun dawo

306

A ranar Larabar nan ne rukunin farko na alhazan Jihar Kano waɗanda suka sauke farali a bana suka sauka a Filin Jirgin Saman Ƙasa da Ƙasa na Malam Aminu Kano.

Majiyarmu ta ruwaito cewa alhazai 534 ne suka bar Filin Jirgin Saman Ƙasa da Ƙasa na Sarki Abdul’aziz dake Jidda a Jirgin Saman Max Air mai lamba Boeing 737 da mislain ƙarfe 10:20 na safe.

Jimillar alhazan Jihar Kano da suka sauke farali a bana sun kai 3,170.

Da yake yi wa manema labarai jawabi a Jidda, Saudi Arabia, Babban Sakataren Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kano, Mohammed Abba Danbatta, ya ce an kammala shirye-shirye tsaf don kammala jigilar alhazan Jihar Kano cikin nasara.

Mista Danbatta ya roƙi alhazan da su zama masu biyayya ga doka musamman wajen ɗakko jakar kaya da ba a so nauyinta ya wuce kilogiram 32, da jakar hannu wadda ba a so ta wuce nauyin kilogiram 8.

Turawa Abokai

1 Sako

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan