Yadda Jami’an Hukumar EFCC Su Ka Yiwa Gidan Tsohon Gwamnan Jihar Lagos Tsinke

94

Jami’an hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta EFCC ta kai wani samame gidan tsohon Gwamnan jihar Lagos, Akinwumi Ambode, a wani bangare na ci gaba da binciken da ake yi masa kan ruf da ciki da dukiyar gwamnati.


Mai magana da yawun EFCC, Tony Orilade ne ya tabbatarwa da manema labarai cewa, Ambode wanda bai dade da sauka daga karaga ba, na fuskantar tuhuma akan cin hanci da rashawa.

Tun da farko dai ana zargin tsohon Gwamnan da bartanar da biliyoyin Naira a tsawon shekaru hudu da ya kwashe yana mulki a jihar, yayin da aka dakatar da asusunsa na banki dauke da makudaden kudade makwanni biyu da suka gabata.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan