Gwamnan Jihar Kogi Ya Ɗaga Darajar Sarakunan Jihar Guda 132

208

Gwamnatin jihar Kogi ƙarƙashin Gwamna Yahaya Bello ta amince da ɗaga darajar Sarakunan jihar guda 132 a dukkanin faɗin ƙananan hukumomi 21 da ke jihar.


Sanarwar ɗaga darajar Sarakunan ta fito ne daga mashawarcin gwamnan jihar na musamman akan ƙananan hukumomi da masarautu na Jihar ta Kogi Mista Abubakar Ohere, in da ya rabawa manema labarai.


Sanarwar ta bayyana cewar an ɗaga darajar Sarakuna 21 zuwa daraja ta ɗaya, sai kuma guda 30 da aka ɗaga darajarsu zuwa daraja ta biyu. Sai sauran 81 da su ka kasance a daraja ta uku.


A karshe sanarwar ta tabbatar da cewa; dukkanin wanda lamarin ya shafa an basu takardun ɗaga darajar ta su, sannan gwamna Yahaya Bello zai miƙa musu sandunan su a makon gobe

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan