Gwamnatin Jihar Akwai Ibom ta ce za rufe makarantun rainon yara, firamare da sakandire fiye da 1,140 dake aiki a jihar ba bisa ƙa’ida ba.
Kwamishinan Ilimin Jihar, Nse Essien, ya bayyana haka a Uyo, babban birnin jihar lokacin da yake ganawa da manema labarai ranar Alhamis ɗin nan.
Mista Essien, wanda fatfesa ne, ya ce manufar shirin rufe makarantun shi ne a dakatar da yaɗuwar makarantu masu zaman kansu marasa izini a jihar.
Ya bayyana rashin jin daɗi bisa yadda mutane marasa kishin jihar ke kakkafa makarantu ba tare da yin rijista da hukumomin gwamnati da suka dace ba.
“Ma’aikatar Ilimi ta Jihar ba ta amince da waɗannan makarantu ba, kuma ana koyar da ɗalibai ne a yanayi na rashin tsafta, inda yanayin koyon yake a taɓarɓare.
“Muna da ƙa’idoji mafiya ƙaranci a Ma’aikatar Ilimi da dole a cika su kafin a buɗe kowace makaranta a jihar nan”, in ji Mista Essien.
Ya ce E Ma’aikatar za ta wallafa sunayen waɗannan makarantu marasa lasisi don al’umma su san su.
Mista Essien ya yi gargaɗin cewa Gwamnatin Jihar za ta gurfanar da masu kunnen ƙashi a gaban kotu.
“Za a wallafa sunayen waɗannan makarantu, daga bisani kuma a rufe su”, in ji shi.