Nan Ba Da Daɗewa Ba Ma’aikatan Ƙasar Nan Za Su Fara Karɓar Mafi Ƙarancin Albashi – Chris Ngige

30

Ministan Ƙwadago Dakta Chris Ngige ya bayyana cewa la’akari da himma da ƙwazonsa ne wajen tattaunawa da ƙungiyoyin ƙwadagon ƙasar nan ya sanya shugaban ƙasa ba shi damar dawowa kan kujerar minista a karo na biyu, ya kuma ce shi da ƙaramin ministan sa za su bakin kokarin su wajen ganin ma’aikatan ƙasar nan sun fara karɓar mafi ƙarancin albashi na ₦30,000 nan ba daɗewa ba.
Ministan ya bayyana hakan ne a gurin liyafar cin abinci da aka shirya a gidansa jim kaɗan da rantsar da shi a matsayin ministan ƙwadago a karo na biyu, ya ƙara da cewa dawowarsa wannan ma’aikata akwai abubuwan da zai fara ta kansu akan lokaci saboda muhimmancinsu.
Ya kuma ce ƙungiyoyi ma’aikatan jami’o’in ƙasar nan da su ke yajin aiki akwai buƙatar daukar matakin da ya dace kuma akan lokaci, saboda irin ƙwarewar aikin da ya ke da ita na tsahon shekaru uku da rabi zai ba shi damar magance matsalar cikin ruwan sanyi.
A karshe ministan ya ce ya himmatu wajen aiki da ƙungiyar ƙwadago ta ƙasa, domin ita ce haɗakar ƙungiyoyin ƙwadago a faɗin ƙasar nan, kasancewar kungiyoyin ƙwadago da su ke ƙarƙashinta su na da yawa, duk da cewa akwai ƙungiyoyin ƙwadago guda 18, amma doka ta iyakance guda 12 kadai waɗanda su ke aiki.

Turawa Abokai

1 Sako

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan