Wani Yaro Ya Nitse A Wani Kududdufi A Kano

188

Wani yaro ɗan shekara 12, Isma’il Safiyanu, ya nitse yayinda yake wanka a wani kududdufi a Sharaɗa Kwanar Maijego a yankin Ƙaramar Hukumar Birnin Kano dake Jihar Kano.

Kaakain Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano, Alhaji Sa’idu Mohammed, ya bayyana haka a Kano ranar Alhamis da safe yayin tattaunawa da Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya, NAN.

Mista Mohammed ya ce al’amarin ya afku ne ranar Alhamis da safe, lokacin da mamacin ya je kududdufin don yin wanka.

“Mun karɓi kiran gaggawa daga wani Malam Jamilu Yahaya da misalin ƙarfe 9:40 na safe, cewa an samu gawar Safiyanu tana kwance a cikin kududdufin.

“Da muka karɓi wannan bayanin, sai muka tura ma’aikatanmu masu ceto zuwa inda abin ya afku da misalin ƙarfe 9:45 na safe.

“An samu Safiyanu a mace, an kuma miƙa gawarsa ga ‘yan sanda a Sharaɗa”, in ji shi.

Turawa Abokai

1 Sako

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan