Ma’aikatan Sahad Stores Da Aka Kora Sun Garzaya Kotu Don Neman Diyya

202

Wasu ma’aikatan Kantin Siyar da Kayayyakin nan, Sahad Stores da aka kora kwanakin baya sun maka tsohon uban gidansu, Alhaji Ibrahim Mijinyawa a kotu suna zargin cewa ya kore su ne ba bisa ka’ida ba.

Idan dai za a iya tunawa, a watan Yuli ne aka kori ma’aikatan Sahad Stores dake Zoo Road da Mandawari har 74 bisa zargin ɓatan wasu kuɗaɗe da suka kai Miliyan 250.

Lauyan masu ƙara, Abba Hikima ne ya shigar da ƙarar a gaban Kotun Ma’aikata ta Ƙasa Reshen Jihar Kano.

Mista Hikima ya shaida wa manema labarai cewa ma’aikatan da aka kora suna nema a dawo da su, a biya su bashin albashinsu, kuma a ba su diyyar Miliyan 250.

Ya ƙara da cewa ana ƙarar Sahad Stores da mamallakinsa, Alhaji Ibrahim Mijinyawa ne a wannan ƙara.

Turawa Abokai

1 Sako

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan